23 Janairu 2020 - 18:12
Rauhani; Iran Zata Mutunta Yarjejeniyar Nukilya

Shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya bayyana cewa, kasarsa tana nan kan bakanta na mutunta yarjejeniyar nukiliya, matukar daya bangaren ya mutunta wannan yarjejeniya.

ABNA24-Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar zaman majalisar ministocin kasar a birnin Tehran, inda ya kara jaddada cewa, ci gaba da aiki da yarjejeniyar nukiliya ya dogara ne kawai da yadda sauran bangarorin yarjejeniyar suka yi aiki da ita.

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin kasar Amurka ta tafka babban kure dangane da ficewar da ta yi daga wannan yarjejeniya ta kasa da kasa, kuma duk abubuwan da suka biyo baya sakama ne na wannan kure da Amurka ta tafka.

Dangane da kasashen turai kuwa, ya bayyana cewa, sun dauki alkawulla ga Iran domin kare yarjejeniyar daga rushewa, amma kuma suna ta jan kafa wajen aiwatar da su, wanda kuma rashin aiwatar da hakan ne zai jefa yarjejeniyar cikin mawuyacin hali, kuma dole ne turawan su dauki nauyin dukkanin abin da zai biyo baya.